30 Nuwamba 2021 - 11:53
Lebanon: Basil Ya Ce Lalacewar Tattalin Arzikin Kasar Shi Ne Babbar Matsalar Kasarsa

Shugaban jam’iya ‘Jam'iyyar Yancin Mutanen Kasa’ Jubron Basil ya bayyana cewa lalacewar al-amuran siyasa ta kasar Lebanon shi ne babbar matsalar da kasar take fuskanta, sannan manufar jam’iyyarsa ita ce kubutar da tsarin tattalin arzikin kasar daga faduwa da wargajewa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Rusiyal Yawm ta nakalto Basil yana fadar haka a shafinsa na twitter a jiya Litinin. Ya kuma kara da cewa maido da kudaden kasar wadanda manya-manyan yan siyasa, yan majalisar dokoki da kuma wadanda suke fada a ji a kasar shi ne babban abinda yakamata a sanya a gaba don kubutar da tattalin arzikin kasar daga rushewa kwatakwata.

Shugaban jam’iyyar ‘Jam'iyyar Yancin Mutanen Kasa’ ya kara da cewa jita jita ta cewa Iran ta mamaye al-amura a kasar Lebanon kariya ce, kuma wata dabara ce ta kwace ikon kasar wanda wasu 'yan siyasa masu fada a ji a kasar suke yadawa don cimma mummunan manufofinsu.

Basil ya kammala da cewa, a irin wannan halin dole ne mutanen kasar su damu, su kuma nuna rashin amincewarsu da yadda al-amura suke tafiya a kasar.

342/